Darus-sahaba
1jojlxKOMkX9WyteRe4hGfd...5Tlzwos6Wa8pU99NjJEjmoO7lE72qs...P8zLBUI5VEdw01bf9Bj3WN2UJZQ0kMkumqAOI9CU319yy4DVw
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka

wanna shafi yana zuwa muku kai tsaye daga masallacin jumu'a
Jami'u Abu hurairah
Dake kurna y'an kifi titin y'an smogal a karamar hukumar dala dake kano Nigeria
kar kashin jagorancin
Sheik Muhammad Sani Uthman Kurna

Home
Karatut-tukan Sheik Muhammad Thani Uthman Kurna
Mata A Musulunci
Bayanin Zakka
Bayanin Azumi
Bayanin Hajji da Umara
Kasuwanci mai ribar gaske
Muhimmin Sako Zuwa ga Ma'aurata
Tsarin Mu'amala A cikin Musulunci
Hakkokin Manzon Allah s a w Akan Alumarsa
Shin hadin kai zai yiwu tsakanin Ahalussunnah da shi a
Wadanna mata aka Haram tawa musulmi da kuma wanda aka Halarta
Hukunce - Hukunce da suka shafi mata
Jinin Al ada ga mata
Jagoran mai wa azi
Adduo in manzon Allah s a w
Falalar Karatun Al-kur'ani
Falalar Sahabbai {R.A}
Falalar Sahabbai {R.A} Daga bakin Imamai
Tarihi
Falalar Ahlulbait daga bakin Ahlussunnah
Tambayoyi masu muhimmanci A cikin Addinin Musulunci
Ayyukan Zuci
Tattaunawa Ta Nitsuwa
Addinin Shi'a
Hukunce-Hukuncen Da Suka Shafi Mata
Karatut-tukan Malamai da Lakcocin su



2014-12-18

-----------------------------------

(KASHI NA BIYU)

JERIN SUNAYEN MATAN DA YA HALATTA MUTUM MUSULMI YA YA AURAE

SU NE KAMAR HAKA:-

1.Diyar mijin mahaifiya wacce ta haifeka

2.Diyar mijin mahaifiya wacce ta shayar da kai nono

3.Matar mijin mahaifiya wacce ta haifeka(in sun rabu)

4.Matar mijin mahaifiya wacce ta shayar da kai nono (in sun rabu)

5.Uwar mijin mahaifiya wacce ta shayar da kai

6.Uwar mijin mahaifiya wacce ta shayar da kai nono

7.Diyar mijin diyar wacce ka haifa

8.Diyar mijin diyarka ta shayarwa

9.Uwar matar danka wadda ka haifa

10.Uwar matar danka na shayarwa

11.Diyar matar danka wadda ta wani miji

12.Diyar matar danka na shayarwa

13.Uwar matar babanka mahaifi

14.Uwar matar babanka na shayarwa

15.Matar dan matarka na cikinta(in sun rabu)

16.Matar dan matarka na shayarwa(in sun rabu)

17.Yar'uwar yar'uwarka wacce kuka hadaa uwa daya da ita,ta hanyar nasaba ko shayarwa

18.Yar'uwar dan'uwanka wadda kuka hada uwa daya da shi

19.Yar'uwar shayarwar dan'uwanka na wata macen daban

20.Yar'uwarka ta shayarwa ta halatta ga dan'uwanka na nasaba

21.Idan wata macen daban ta shayar da yar'uwarka ko dan'uwanka nono,to kai ya halatta ka aureta

22.idan wata mace daban ta shayar da dan'danka nono,to kai ya hakatta ka aureta

23.Idan wata macen daban ta shsyar da dan cikinka nono,to kai ya halatta ka aurota

24.Idan wata mace daban ta shayar da danka nono,to kai ya halatta ka aurota

25.Idan wata mace daban ta shayar da danka,to kai ya halatta ja auri matar

26.Idan wata mace daban ta shayar da kawunka ko gwaggonka nono,to kai ya hakatta ka aureta

27.Idan wata mace daban ta shayar baffanka ko innanka wato yar'uwarsa,to kai ya halatta ka aureta

28.Uwar jikanka na shayarwa ya halatta ka aureta

29.Ya halatta ka auri kakar jaikanka na shayarwa

30.Ya halatta ka auri jajar danka na shayarwa

31.Ya halatta ka auri kakar danka na shayarwa

32.Ya halatta ka auri gwaggon danka na shayarwa

33.Ya hakatta ka auri mata majin diyarka

34.Ya halatta ka auri matar gwaggon danka na shayarwa

35.Ya halatta mace ta baban dan'uwanta na shayarwa

36.Ya halatta mace ta auri,uban jikanta na shayarwa

37.Ya halatta mace ta auri,jakan jikanta na shayarwa

38.Ya halatta ka auri,kakar danka na shayarwa

39.Ya hakatta ka auri,uwar matar da ta shayar da danka

40.Ya halatta ka auri,diyar matar da ta shayar da danka

41.Ya halatta ka auri,diyar matar da ta shayar da dan'dan uwanka ko yar'uwarka

42.aYa halatta ka auri,matar da ta shayar da jikarka

43.Ya halatta ka auri,matar kakanka wadda kuke ciki daya ko uba daya ko uwa daya ko da yana da rai,haka shima zai iya aurar taka ko kana da rai kaima(Indai auren na baya ya rabu)

44.Ya halatta ka auri,matar wan babanka ko yana da rai(in sun rabu)

45.Ya hakatta ka auri,matar dan'uwan babarka koda yana da rai(in sun rabu)

WADANNAN SU NE JERIN GWANON MATAN DA YA HALATTA,MUSULMI YA AURA.

ALLAH SHI NE MASANI.

DAGA

DAN'UWANKU

ABDULMAJID IBN NUHU

DA MASU TAIMAKAMIN

MALAM ADAMU KABIRU YARGAYA

MALAM AWAISU AL'ARABEE FAGGE

MALAM SANI USMAN KURNA

MALAM DR. JAMILU ZAREWA

MALAM BASHIR JOURNALIST

MALAM NAZIFI KABIRU

MALAM AHMAD IBN TAIMIYYAH

DA SAURAN MALAMAI WADANDA,BAZA SU IRGU ANAN BA

DA KU MASU BIBIYATA

ALLAH YA SAKAWA KOWA DA AKKHAIRI,YA KARA MANA IKLASI,AMIN.


MATAN DA MUSULUNCI YA HANA KA,KA AURA DA KUMA WADANDA YA YARDA KA AURA.

An karbo daga Ummu habibata R.A yar abu sufyan R.A cewa "YA MA'AIKIN ALLAH SAW mai zai hana ka auri yar'uwata diyar abu sufyan mana?"

sai MANZON ALLAH S.A.W yace da ita "YANZU KINA SON HAKA?"

sai na ce da shi S.A.W "ee zan so hakan mana tunda ni nasan ba zai yiwu na zauna da kai ni kadai ba,don haka haka kuwa duk wani wanda zai yi tarayya dani a kanka,ai na fi son yar'uwata ta yi tarayya dani(a kanka).

BUKHARI ya rawaito shi a hadisi mai lamba 5101/43/9 ,5106,5107,5123

MUSLIM ya rawaito shi a hadaisi mai lamba ta 26,25,10,4

Su matan da aka haramtawa musulmi ya aura sun kasu kashi kashi NA FARKO sun haramta ya aure su har abada,NA BIYU kuma sun haramta ya auresu ne na wani lokaci.

KASHI NA FARKO

WADANDA SUKA HARAMTA A AURESU HAR ABADA,SU NE KAMAR HAKA:-

1.Uwar mahaifiya da mahaifiyarta har ya zuwa ba iyaka.

2.Yar'tsatso da diyarta da itama diyar har ya zuwa ba iyaka.

3.Yar'uwa shakikiya

4.Yar'uwa li'abbiya.

5.Yar'uwa li'ummiya

6.Yar yar'uwa

7.Yar yar'uwarka wadda kuke uba daya

8.Yar yar'uwa wadda kuke uwa daya

9.Yar dan'uwanka shakiki

10.Yar dan'uwanka wanda kuke uba daya

11.Yar dan'uwanka wanda kuke uwa daya

12.Kanwar babanka shakikiya

13.Yar mahaifi shakikiya

14.Yar%mahaifi wacce suke uba daya

15.Yar'mahaifi wacce suke uaw daya

16.Yar'uwar mahafiyarka shakikiya

17.Yar'uwar mahaifiyarka wacce suke uba daya

18.Yar'uwar mahaifiyarka wacce suke uwa daya

19.Mahaifiyar matarka

20.Kakar matarka har zuwa ba iyaka

21.Diyar matarka(agola)

22.Jikar matarka(diyar yar'ka,wato agolarka)

23.Matar mahaifinka

24.Matar kakanka(na wajen uwa ko uba)

25.Matar danka na cikinka

26.Matar jikanka komai nisansa

27.Diyar yar'ka(jikarka)

28.Jikar yarka duk nisanta

29.Babarka ta shayarwa

30.Kakarka ta shayarwa

31.Yarka ta shayarwa

32.Kanwarka ta shayarwa

33.Diyarka ta shayarwA

34.Jikarka ta shsyarwa

35.Gwaggonka ta shayarwa

36.innarka ta shayarwa

37.Matar da akwai aure a kanta(matar wani)

WADANNAN SUNE MATAN DA SUKA HARAMTA A GAREKA KA AURE SU,HARAMCI NA HAR ABADA.

KASHI NA BIYU

AMMA SU KUWA MATAN DA YA HARAMTA KA AURE SU NA WANI LOKACI SU NE KAMAR HAKA:-

1.Yar'uwar matarka da kuke tare da ita

2.Innar matarka da kuke tare da ita

3.Gwaggon matarka da kuke tare da ita

4.Matar da ake son a aura kafin mace ta hudu 4 da aka saka ta gama iddah

5.Mazinaciya har sai ta tuba

6.Matar da aka saka saki uku ko sau uku har sai tayi wani auren

7.Matar da ta yi haramar ga hajji ko umara har sai ta kammala

8.Mai iddar wani har sai ta gama

WADANNA. SU NE MATAN DA YA HARAMTA A AURE SU NA WANI LOKACI NA WANI LOKACI.

MATAN DA YA HALATTA MUSULM YA AURA.

ALLHA YASA MUDA CAI NAN GA BA ZA MU KAWO MUKU MATAN DA YA HA LARTA KU AURA.

ABDULMAJID IBN NUHU




Kuna iya tuntu6ar mu ta wadannan hanyoyin
Abdul-majid Ibn Nuh ta face book

KO TA SHAFIN MU NA FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI TA FACE BOOK.

Ko ta watsAp A 07063276717
Bugo mana waya ta nan
Bugo mana waya ta nan
Bugo mana waya ta nan
Ko ta Email A

Home


Copyright © 2014 - 2015By:- Abul-majid Ibn Nuoh Powered by- Basheer journalist sharfadi


Snack's 1967